A sanarwa da ministan labarai Lai Muhammed ya fitar ranar talata a garin Abuja, mai baiwa shugaban kasa shawara Kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya kafa wannan kwamitin.
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti tax musamman wanda zata yi bincike kan yan matan makarantar Dapchi da mayakan boko haram suka sace.
A labari da Sahara reporter ta fitar za’a kaddamar da kwamitin Wanda ya kunshi mutum 12 ranar laraba 28 ha wata.
A sanarwa da ministan labarai Lai Muhammed ya fitar ranar talata a garin Abuja, mai baiwa shugaban kasa shawara Kan harkokin tsaro Babagana Monguno ya kafa wannan kwamitin.
Kwamitin dai zata samu jagoranci na babban jami’in sojoji Nijeriya wanda ya kai matsayin manjo janar.
Kwamitin zata kunshi jami’o’i daga rundunar sojan Sama da kasa har da na ruwa. Ciki har da dan sanda da yan sandan farar hula da jami’in civil defence Tare da jami'o'i guda biyu daga gwamnatin jihar Yobe.
Daga bisani kwamitin zata yi bincike kan yadda yan ta’adar suka samu nassrar far ma garin haka kuma zata bada hanyoyi da za'a bi wajen kubitar da yan matan da yan ta'adar suka yi awon gaba dasu.
A kwanan baya yayin da ya zanta da manema labaraia a daidai makarantar yan matan da aka sace, ministan yana cewa gwamnatin tarayya tana iya bakin kokarin ta wajen kawo karshen ta'addancin kungiyar tare da yin la'akari na cewa harin da suka kai yankin yana iya zamantowa borin kunya kasancewa sojoji sun fatattaki asalin gidauniyar su dake nan dajin sambisa.