Yan matan Dapchi: Ku daina nuna yatsa ga juna, Dogara ya gargadi sojoji da yan sanda.

Buhari felicitates with House Speaker, Dogara at 50

Kakakin ya lura da sa-in-sa da jami’o’i tsaro keyi game da yan matan makarantar Dapchi da mayakan boko haram suka sace.

Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya gargadi rundunar sojoji da yan sanda da su suyi Watsi da zargin da suke ma juna.

Kakakin ya lura da sa-in-sa da jami’o’i tsaro keyi game da yan matan makarantar Dapchi da mayakan boko haram suka sace.

A bisa rahotanni da aka fitar, jami’o’i suna zargin juna da sakachi wanda ya kai har yan ta’adar suka far ma al'ummar Dapchi.

A wata takardar sanarwa da kakakin ya fitar ma manema labarai ranar talata 27 ga wata, ya gargadi hukumomin tsaron da suyi watsi da zargin da suke ma juna kuma su hada kai wajen tabbatar yan matan sun dawo ga kawunan su.

Yana mai cewa “ baza mu lamunta da irin hakan. Majalisar wakilai da ma yan Nijeriya Baki daya zasu daura alhakin ga jami’an tsaro. Zasu bada amsa ga wannan abun bakin ciki da ya faru".

Kakakin yayi.amfani da damar wajen jajanta ma iyayen yan matan makarantar Dapchi da aka sace da ma jama’ar bisa abun takaici da ya faru.

Daga karshe kakakin ya roki yan kasar dasu cigaba da yin addu’o’i don ganin yan matan sun dawo ga iyalen su.

A ranar 19 ga watan febreru yan ta'ada wanda ake zargin cewa mayakan boko haram ne suka kai harin garin Dapchi har suka yi nasarar kubita da yan matan sakandare dake nan garin.

Post a Comment

Previous Post Next Post