Justice Aloycious Katsina-Alu: Shugaba Buhari yayi jimamin mutuwar tsohon mai sharia

Ex-CJN, Aloysius Katsina-Alu, is dead at 76

Tsohon mai shari'ar ya rasu ne ranar Laraba 18 ga watan Yuli a wata asibiti dake garin Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Bada dadewa bayan saukar sa kasar daga kasar Netherland, shugaba Muhammadu Buhari yayi jimamin mutuwar tsohon alkalin alkalan Nijeriya Justice Aloysious Katsina-Alu.

Tsohon mai shari'ar ya rasu ne ranar Laraba 18 ga watan Yuli a wata asibiti dake garin Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

labarin mutuwar tsohon alkalin mai shekaru 76 a duniya ya fito ne a wata takardar sanarwa da kakakin shugaban alkalai na kasa ya fitar.

A wata takardar sanarwa da kakakin shugaba kasa Garba Shehu ya fitar ranar laraba 18 ga wata a garin Abuja, shugaban yayi jimmamin mutuwar marigayin.

Shugaban ya isar ma iyaken sa da gwamnatin jihar Benuwe har ma da kungiyar alkalan Nijeriya da sakon ta'aziya.

Shugaban ya jinjina ma margayin yace yana daya daga cikin kwararrun alkalai da suka taka rawar gani wajen sauya tsarin shari'ar ta kasa.

Yace babu tantama tambarin da tsohon alkalin alkalan Nijeriya ya bari zata zamanto abun koyi ga sauran alkalai masu tasowa.

Daga karshe shugaban yayi masa Addua tare da yi ma iyaken da ya bari fatan samun hakurin jure rashin sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post