Rarara ya samu matsayin shugaban harkokin waka a kwamiti mai goyon bayan zarcewar shugaban kasa a zaben 2019.
Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya samu sabon matsayi a cikin wata kwamiti da aka kafa na yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari.
Fadar shugaban kasa karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayye ta nada shi a matsayin shugaban harkokin waka a kwamiti mai goyon bayan zarcewar shugaban kasa a zaben 2019.
Rarara, yana daya daga cikin mawakan arewa da suka tallafawa yakin neman zaben shugaban a zaben 2015.
Wakokin da ya hada yayi yawo sosai gabanin zaben da shugaba Buhari ya samu galaba.
A cikin takardar sanarwa da hadimin shugaban kasa kan harkokin siyasa, Gideon Sammani, ya fitar tsohon gwamnan jihar Borno kuma tsohon shugaban jam'iyar PDP Ali Modu Sheriff zai jagoranci kwamitin.
Duk a cikin sabuwar kwamitin, shima shaharraren dan wasan kwaikwayo a masana'antar Nollywood kuma dan majalisar wakilai a jihar Legas, Desmond Elliot shine aka nada a matsayin sakataren tafiyar.
Kwamitin ya hada da mambobi 35 da wasu manyan masu bada shawara 10 da iyaye masu hannu da shuni biyar.
Kwamitin ya sha bambam da kungiyar yakin neman zaben Buhari ta Buhari Campaign Organisation wanda Rotimi Ameachi ke jagoranta kuma sahararren alkali, Festus Keyamo ke rike da matsayin kakaki.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an kafa kwamitin ne bayan taron kasa da aka gudanar ta jam'iyar APC kwanan baya.
Manufar kafa kwamitin shine domin karfafa manufar jam'iyar tare da kokarin samad da nasara a zaben nan gaba.