Atiku Abubakar: Zan mayar da Adamawa jihar PDP - inji tsohon mataimakin shugaban kasa

Nigeria's security is broken - Atiku Abubakar

Ya tabbatar da hakan ne a garin Yola ranar asabar 21 ga watan Yuli yayin da yake jawabi a taron jam'iya reshin jihar ta shirya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace zai mayar da jihar Adamawa karkashin shugaban jam'iyar sa ta PDP.

Ya tabbatar da hakan ne a garin Yola ranar asabar 21 ga watan Yuli yayin da yake jawabi a taron jam'iya reshin jihar ta shirya.

Atiku yace asali jihar ta PDP ce kuma zaiyi iya bakin kokarin sa wajen mayar da ita karkashin jagorancin ta.

Ya kaddamar da kansa a matsayin dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 a wajen taron.

Jigon ya nuna mamakin sa bisa daruruwan mutane da suka halarci taron inda danganta haka ga farin jinin da PDP take da shi a jihar,

Tsohon jigon jam'iyar APC ya soki gwamnatin jam'iyar adawa ta APC dake mulki kan rashion samad da cigaba a fanin harkar kasuwanci da tsaro tare da samad da ayukan yi. Yace idan ya hau karagar mulki zai magance wadandan matsaloli.

Wannan ya kara tabbatar da maganar da yayi kwanan baya na kawo karshen ta'adanci a kasar.

A jawabin sa wajen taron sa da magoya bayan sa a jihar Borno, Atiku Abubakar ya sha alwashin kawo karshen ta'adanci Boko Haram da sauran yan ta'ada a kasar idan ya hau kujerar mulki.

Post a Comment

Previous Post Next Post