
Jarumin tawagar super eagles shine dan wasa a tarihin tawagar yan kwallon Nijeriya wanda ya samu nasarar zura kwallo mafi yawa a gasar kofin duniya.
Jajirtaccen dan wasan gaban tawagar super eagles na Nijeriya, Ahmed Musa, ya kafa tarihi bayan kwallayen da ya zura a raga wasan Nijeriya da Iceland a gasar kofin duniya.
Jarumin tawagar super eagles shine dan wasa a tarihin tawagar yan kwallon Nijeriya wanda ya samu nasarar zura kwallo mafi yawa a gasar kofin duniya.
Ahmed Musa yana rike da wannan tarihin ne bayan da ya taimaki Nijeriya da zura kwallo biyu a raga wasan ta da Iceland wanda aka tashi 2-0.
Da hakan dan kwallon yana da kwallo hudu a tarihin gasar ma tawagar super eagles. Ya samu kwallo biyu a gasar wasan su da Argentina a gasar 2014.
Banda na Nijeriya, dan kwallon shine dan wasan kungiyar Leicester na kasar Ingila da zai fara zura kwallo a raga a a tarihin gasar kofin duniya.
Kai ga yanzu yan Nijeriya yan Nijeriya suna cigaba da nuna farin cikin su bisa sakamakon wasan yau. Wasu da dama suna jinjina ma Ahmed Musa game da yadda ya jajirce a wasan kuma ya fitar da kasar daga kunya.