Cikin masu taya murna akwai fitatun jarumai na ko wani masana'anta dake kasar. Ga yadda jarumin masana'antar Kannywood, Adam A.Zango yayi nashi murnar
Bayan wasan ta da kasar Iceland wanda aka tashi 2-0, yan Nijeriya sun kasa boye farin ciki dake tattare dasu sakamakon wasan cikin su har da Adam Zango.
Nijeriya dai ta lallasa abokan adawar ta wasan ta na biyu a gasar kofin duniya kuma Ahmed Musa shine jarumi wanda ya ceci kasar bayan ya zura kwallaye biyu a wasan.
Yan Nijeriya dai kai ga yanzu suna cigaba da murna yayin sakamakon wasan ya zama abun muhawara a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labarai.
Cikin masu taya murna akwai fitatun jarumai na ko wani masana'anta dake kasar. Ga yadda jarumin masana'antar Kannywood, Adam A.Zango yayi nashi murnar
Jarumin ya wallafa faifan bidiyon a shafin sa na Instagram bayan jerin sakonin da ya fitar na taya murna.
Kamar yadda za'a gani a bidiyon jarumin yana kwaikwayan rawar Shaku-shaku wanda mamaye ko wace rawa a Nijeriya halin yanzu.