Yayin da yake taka leda a Juventus, Lichtsteiner yayi nasarar daga kofin firemiya na Italiya sau bakwai tare da sauran kofunan kasar da dama.
Sabon kociyar kungiyar Arsenal, Unai Emery ya shigo da zafi-zafi inda ya fara siyan dan wasan baya kasar Switzerland zuwa kungiyar da taka leda.
Stephan Lichtsteiner mai shekaru 34, tsohion dan wasan kungiyar Juventus ne dake kasar Italiya.
Dan wasan wanda ya rattaba hannu ga neman da Arsenal tayi mashi bayan karewar kwantiragin sa da tsohon kungiyar shi ya shigo kungiyar gabanin fara sabuwar kakar firemiya.
Yayin da yake taka leda a Juventus, Lichtsteiner yayi nasarar daga kofin firemiya na Italiya sau bakwai tare da sauran kofunan kasar da dama.
Sabon kociyar Arsenal ya bayyana dalilin da ya sanya ya fara siyo dan wasan gabanin sauran yan wasa inda yake cewa "Lichsteiner kwararre ne kuma yana da basirar kwallo".
Unai Emery yace dan wasan zai taimaki sauran yan wasan kungiyar da irin basirar da yake dashi da kwarewarsa.
Dan wasan wanda zai jagoranci kasar sa Switzerland a gasar cin kofin duniya zai saka lamba 12 na rigar Arsenal bayan karewar gasar duniya.
Ana sa ran cewa wata kila ya maye gurbin Hector Belerin a baya ko kuma a sauya masa matsayi zuwa tsakiya kasancewa yana iya rike matsayin ba tare da wata haufi ba.