Shugaban kasa ya shirya liyafar bude baki ma sarakunan gargajiya da malaman nijeriya a fadar sa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya liyafar bude bakin azumin ranar 20 ga watan azumi a fadar sa inda ya gayyaci sarakunan gargajiya da malaman Addini.
Manyan sarakunan gargajiya na ko wani yanki sun halarci liyafar wanda aka shirma masu musamman tare da manyan malaman addinin musulunci dake kasar.
Shugaban ya halarci taron liyafar tare da shugaban mai'aikatan fadar sa, Abba Kyari da wasu ma'aikatan fadar sa.
Tags:
News