Dan wasan Liverpool yayi nasarar saka kwallo daya a raga sanadiyar fenerti da suka samu, sai dai hakan bai fishe su ba inda aka tashi 3-1 galabar ga Rasha.
Wasan su na biyu da kasar Rasha, yan wasan masar sun gamu da abun takaici inda abokan adawan su suka zura kwallaye uku a raga.
Duk da dawowa fitaccen dan wasan gaban ta, Mohamed Sallah, wanda bai samun 7a bugta wasan su na farko sakamakon raunin da ya samu, hakan bai taimake su wajen tsallakewa zuwa rukuni na biyu na gasar kofin duniya.
Dan wasan Liverpool yayi nasarar saka kwallo daya a raga sanadiyar fenerti da suka samu, sai dai hakan bai fishe su ba inda aka tashi 3-1 galabar ga Rasha.
Wasa na biyu kenan cikin uku, yan kasar Masar suka yi rashin nasara. Da wannan babu tantama kasar tana cikin shirin dawowa gida.
Wasan su na farko da Uruguay yan kasar arewacin Afrika sunyi rashin dace inda dab da karshen wasan Jose Gimenez ya zura kwallo mai ban haushi a ragar golan Egypt.
A gasar dai na bana, tawagar kasashen Afrika suna cigaba da fuskanta barazana amma banda Senegal wanda ta zama kasar Afrika da tayi nasarar doke abokan adawar su wasun su na farko a ciklin rukunin su.
Kasar yammacin afrika ta doke Poland 2-1 da taimakon dan wasan kungiyar Everton, Idrissa Gueye da M'baye Niang.