Gabanin wasan Senegal, kasashen Afrika dake fafatawa a gasar bana kama daga Egypt, Moroko, Nijeriya da Tunisia duk sunyi rashin dace wasan su na farko a gasar bana.
Yayin da sauran kasashen Afrika suka fuskanci zagon kasa a wasannin zangon farko, Senegal ta ware kanta daga shiga sahun su inda tayi nasarar doke kasar Poland.
Wasan su a yammacin ranar talata 19 ga watan yuni, Kasar yammacin afrika ta doke Poland 2-1 da taimakon dan wasan kungiyar Everton, Idrissa Gueye da M'baye Niang na kungiyar AC milan.
Gabanin wasan Senegal, kasashen Afrika dake fafatawa a gasar bana kama daga Egypt, Moroko, Nijeriya da Tunisia duk sunyi rashin dace wasan su na farko a gasar bana.
Yan wasan Senegal sun nuna bajinta da jajircewa wanda da hakan sauran yan kasashen afrika ke murnar nasarar su a kafafen sada zumunta.
Gasar bana dai, Egypt ta kasance kasar Afrika ta farko da aka tabbatar rashin samun damar ketara zuwa rukuni na biyu bayan da Rasha ta doke ta wasan ta na biyu.
Duk da fitacen dan wasan gaban ta, Mohammed Sallah, yan kasar Masar sun ci karo dodon su a wasan wanda aka tashi 3-1 nasara a madadin abokan adawan ta.
Wasan dai, Sallah, ya samu damar zura kwallo daya a ragar rasha sakamakon Fenarti da suka samu, sai dai wannan bai yi ceci su wajen yin nasara.