Ahmad Makarfi: Tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana aniyar sa na tsayawa takarar shugaban kasa

Ex-PDP caretaker chairman, Ahmed Makarfi to run for President

Tsohon shugaban jam'iyar na rikon kwarya, ya bayyana cewa ya dau matakin fitowa takarar bayan shawara da ya nema daga wasu abokan sa.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jigo a jam'iyar adawa ta PDP, Ahmed Makarfi, ya bayyana aniyarsa na tsayawa takara a zaben 2019.

Tsohon shugaban jam'iyar na rikon kwarya, ya bayyana cewa ya dau matakin fitowa takarar bayan shawara da ya nema daga wasu abokan sa.

Kamar yadda ya shaida ma manema labarai, yana dab da siyan katin neman zabe karkashin jam'iyar PDP.

Matakin nasa ya biyo bayan fitar da jadawalin sharuda da jam'iyar sa ta fitar ga masu neman tsayawa takara.

Bisa ga jadawalin yan takara zasu biya naira miliyan N12M na katin neman kujerar shugaban kasa.

Bugu da kari, mata masu niyar neman kujera mulki zasu siya kati a kan Naira miliyan N2M kana su samu katin tsayawa takara kyauta.

Post a Comment

Previous Post Next Post