Boko Haram: Saurari sakon da ma'aikaciyar jin kai ta fitar yayin da mayakan boko haram ke kokarin sace ta

'We're under attack, pray for me', Boko Haram victim speaks

Mai'aikaciyar mai suna Hauwa Liman Muhammed ta bukaci a sanar ma iyayenta cewa yan boko haram sun kwo masu hari inda take aikin jin kai

Wata ma'aikaciyar kungiyar jin kai mai suna Hauwa Liman Muhammed ta tura sakon fargaba yayin da boko haram ke kokarin saceta sakamakon harin da suka kai garin Rann dake jihar Borno.

A cikin sakon da ta tura ma abokin ta ta hanyar Whatsapp hauwa cikin fargaba da tashin hankalin ta bukaci shi da ya sanar ma wata Fatima da iyalen ta cewa yan ta'adda sun kawo masu hari.

Cikin kuka ita dai wannan baiwar Allah bata so a sanar da iyayen ba domin bata son hankalin su ya tashi.

 

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! ka kira fatima ka gaya ma iyayen na amma kar ka gaya masu yanzu. boko haram sun shigo inda nake.

"ina tsoro kada ka gaya masu yanzu. idan iyaye na suka ji b aza su ji dadi ba. Wallahi ina tsoro" ta sanar cikin fargaba.

Cikin kokarin da take wajen fitar da sakon za'a ji inda take ihu yayin da yn ta'adar suka shiga inda take.

Mayakan Boko Haram sun kai hari a sansanin sojojin Najeriya dake garin Rann cikin jihar Borno ranar alhamis 1 ga watan Maris.

Yan Boko Haram din sun kashe sojojin da wasu yan sanda dake tsaron sansanin kana suka sace wasu ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ciki har da Hauwa Liman.

Post a Comment

Previous Post Next Post