Yan sanda sun kama shi a jihar Nasarawa tare da da wasu mabiyan shi su uku tare da wasu bindigogi
Tawagar jami'an ta musaman na fanin amfani da basira ta hukumar yan sanda sun kama babban jagora kuma wanda ake zargi da shirya hare-haren da wasu yan hana ruwa gudu suka kai jihar Benuwe wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 73.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, an kama jagorar kungiyar yan ta'addar mai suna Alhaji Laggi kuma mai shakaru 40 a yankin garin Tunga dake jihar Nasarawa.
Banda shi yan sandan sun kara kama wasu mabiyan kungiyar su uku Mumini Abdullahi da Muhammed Adamu da Ibrahim Sule.
Sun amsa laifin aika-aikar da suka aiwatar a jihar Benuwe wanda ya sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami'an tsaro.
An kama su tare da wasu bindogi kerar Ak47 da wasu makamai tayar da fitina.
Jami'an tsaron sun gabatar da shiri na musamman a jihohin Benuwe da Nasarawa da Taraba domin kawo karshen hare-haren dake faruwa a cikin jihohin.
Wannan kamun ya biyo bayan rahoton da kwamishnan yan sanda na jihar Banuwe Fatai Owoseni yayi ranar 1 ga watan yau na cewa an kama wasu mutane 4 da ake zargin cewa suna da hannu game da rikicin da ya faru a jihar.