Kashe-kashe a jihar Zamfara: An kama mutum uku kan kashe-kashe da ya faru a Zamfara

Zamfara Killing: Police confirms arrest of 3 suspects
A wata sanarwa da kakakin hukumar CSP Moshood Jimoh ya sa hannu, hukumar ta sanar cewa wadanda aka kama suna bada hadin kai wajen cigaba da bincike kan aika-aikar da ya faru.

Hukumar yan sanda ta kama wasu mutune uku da take zargin da sa hanu kan kashe kashe da ya faru a garin Birane na karamar hukumar Zurmi na jihar Zamfara kwanan baya.

A wata sanarwa da kakakin hukumar CSP Moshood Jimoh ya sa hannu, hukumar ta sanar cewa wadanda aka kama suna bada hadin kai wajen cigaba da bincike kan aika-aikar da ya faru.
Wadanda aka kama sun hada da Halilu Garba mai shekara 45 da Zubairu Marafa mai shekara 45 da Nafi’u Badamasi mai shekara 40.

Za'a gurfanar dasu gaban kotu bayan kammala bincike kamar yadda kakakin hukumar ya sanar.
Wannan kamu ya faru bayan baban sufeton yan sanda Idris Ibrahim ya tura wasu dakaru zuwa jihar domin dakile hare-hare dake faruwa a jihar.
A ranar alhamis 15 ga watan febreru 2018 yan bindiga suka kai hari hari garin  Birane har suka kashe mutum sama da 41.

Post a Comment

Previous Post Next Post