Matasan sun bayyana cewa basu san abubuwa da zasu da kudin idan sun same shi amma daya daga cikin abubuwan da zasu fara yi shine siyan a daidaita tsahu
Hukumar yan sanda ta jihar Kano ta kama wasu matasa wadanda suka sace wani yaro dan shekara hudu tare da neman kudin fansa na miliyan 2.
Matasan Jabir Usman Sule da Bashir Aminu, sun sace yaro a daidai garin Dorayi kana suka bukaci iyayen shi da su biya miliyan 2 kafin su sake shi.
kamar yadda jami'in yan sanda ya sanar, sun shiga hannu ne ta hanyar wasikar da suka tura ma dan uwar yaron da suka sata.
Yayin da suke bada amsar tambayoyi daga manema labarai, matasan sun bayyana cewa basu da hakikanin abun da zasu yi da kudin idan har sun samu nasarar samun amma daya daga cikin abun da zasu fara siya shine a daidaita tsahu wato keke mai kafafu uku.
Tags:
News