Siyasar Kano: Yan Kwankwasiya da Gandujiya sun gwabza a jihar Kano, mutum 6 sun rasu

Anyi jina jina tsakani yan kwankwasiyya da gandujiya

Lamarin ya faru ne a wani daurin aure da mabiyan yan siyasar suka halarta a nan garin Kano

Magoyan bayan tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ta da na gwamnan yanzu Abdullahi Umar Ganduje sun gwabza a jihar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 6.

Rahotanni ya nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da mabiyan suka halarci wani taron daurin aure a nan garin Kano.

*Hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Kwankwaso

Jami'in dake hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar Magaji Majia ya tabbatar da aukuwar gumurzun tare da shaida wa manema labarai cewa hukumar ta fara bincike akan lamarin.

 

Wannan dai ya faru bayan yan kwanaki da kwamishnan ayuka ta musamman na jihar Alhaji Abdullahi Abbas yayi wasu kalaman batanci ga yan akidar kwankwasiyya a wata faifon bidiyo.

Gwamnan jihar kano ya sha da ƙyar harin da ƴan fashi suka kai mai

*Cikin bidiyo dake nan kasa, kwamishnar yayi barazana na a jifi mabiyan tsohon gwamnan jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post