Shugaban Muhammadu Buhari: Ya dace shugaba Buhari ya zarce da shugabanci - inji Garba Shehu

Shugaba Muhammadu Buhari ( daga Bayo Omoboriowo)

Shi dai Kakakin bai sanar ko shugaban zai zayyana anniyar yin takara a zaben 2019 amma yana mai la'akari cewa bisa ga irin ayyuka da shugaban ya gudanar zai sanya jama'a su amince da zarcewan shi.

Babban mataimakin shugaban kasa na bangaren yada labarai Garba Shehu yace ya kamata shugaban ya zarce kan karagar mulki domin sauya harkar shugabanci a kasar.

Kakakin ya sanar da haka a wata hira ta musamman da yayi da gidan telibijin ta Gatefield Television ranar litinin 18 ga watan disamba.

 

Shi dai Kakakin bai sanar ko shugaban zai zayyana anniyar yin takara a zaben 2019 amma yana mai la'akari cewa bisa ga irin ayyuka da shugaban ya gudanar zai sanya jama'a su amince da zarcewan shi.

yana mai cewa "Ya dace Buhari ya zarce da shugabanci bisa ga irin kokarin da yake wajen sauya tunani da halayyar mutane a kasar, domin sai da haka za'a samu gyara a kasar wanda a da tana fama da batutuwan cin hanci da rashawa a ko ta ina. wannan shine abun da shugaba ke kokarin canjawa, kawar da cin hanci da rashawa a kasar.

Shehu ya yaba ayyukan cigaba da shugabanci Buhari ta samu musamman a fannin tsaro  da noma inda yake cewa fannin ta samu cigaba tun kafin a rantsar dashi ofishin sa.

"inda ba Buhari ba da yanzu Boko haram ta mamaye Aso rock da ma garin Abuja haka zalika ba za ki samu damar tattaunawa dani a halin yanzu domin da sun mamaye ko ina. Boko Haram har sun kai yankin Ibadan da jihar Legas.

"mutane na cewa babu ayyukan cigaba da kasar ta samu amma tambaya anan shine akwai yadda za'a gina abun alheri ba tare da an tabbatar da zaman lafiya a kasar?

"A da ana kashe Dala miliya biyar ko wani rana domin shigowa da shinkafa kasar amma a halin yanzu an daina yin haka. Shin mai aka sa ran zamu kara fadi

"mun samad ayyukan yi ga matasa wadanda suka kammala karatu adadin 500,000 ta hanyar tsarin N-Power da makamancin haka.

- Muna bayan shugaba Buhari

Matsayin da ake ciki game da takarar shugaban

A kwanan baya a samu wasu fostoci a garin Abuja na yakin neman zabe na shugaba Buhari da mataimakin sa Osinbajo na zaben 2019.

Duk da cewa shugaban bai bayyana anniyar sa ba akwai kamshin yiuwar haka nan ba da dadewa ba bisa ga maganganu da shugaban yayi kwanan baya.

Yayin da yake ganawa da yan Nijeriya mazaunin kasar Cote D'ivoire shugaban yace ya ziyarci wajen taron ne tare da wasu gwamnoni biyu domin yin haka zai taimaka wajen yakin neman zabe nan gaba.

Hakazalika yayin da ziyarci jihar Kano kwanan baya shugaban yayi tsokaci game da dimbin mutane da suka tarbe shi inda yake cewa " ina cike da farin ciki ganin dimbin jama'a da suka tarbe ni, da wannan na san idan aka gudanar da zabe a halin yanzu hakika zan ci nasara."

Post a Comment

Previous Post Next Post