Mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ya jagoranci sauran jama'a zuwa fadar shugaban tare da yi masa wakar farin ciki na zagoyowar wannan ranar.
Dinbim masu ruwa da tsaki a harkar siyasar Nijeriya sun taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murna zagayowar ranar haihuwar shi.
Jigan-jigan sun ziyarci fadar shugaban kasa jiya lahadi 17 ga watan disamba domin taya shugaban murna zagoyowar wannan ranar mai muhimmanci a rayuwar shi.
Mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ya jagoranci sauran jama'a zuwa fadar shugaban tare da yi masa wakar farin ciki na zagoyowar wannan ranar.
Manyan baki da suka halarci fadar Villa sun hada da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da jigon jam'iyar APC Bola Tinubu.
Hakazalika suma gwamnonin jihar Oyo, Ogun, Imo, Jigawa, Nasarawa, Sokoto, Kaduna, Zamfara, Bauchi, Kebbi da Kogi sun garzaya fadar domin taya jagoran kasar Nijeriya kuma shugaban su murna.
Suma yan majalisar shugaban ba'a baro su baya wajen taya shugaban murna a gangamin bikin wanda aka gudanar bada sanin shuagan domin nuna masa muhimmancin wannan ranar wanda yin haka ya ba shugaban mamaki.
Attajiri dan kasuwa kuma shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ziyarci fadar Villa inda shima ya taya shugaban murna tare da mika masa katin taya murna.
Sauran jama'a basu gaza ba wajen taya shugaban murna inda dinbim jama'a suna ta mika sakon taya murna a shafukan su ta kafafen sada zumunta ga shugaban.