
Za'ayi nadin sarautar mawakin ranar 27 ga watan Disemba a fadar sarkin Kano.
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi Na biyu zai nada shahararen mawakin Hausa Nazir M.Ahmad a matsayin Sarkin wakar sarkin kano.
Labarin haka ya fito ne a cikin wata takarda da Danburan Kano, Munir Sanusi ya fitar Ranar 28 ga watan Nuwamba.
Sanarwar tana mai cewa "Mai marataba Sarkin Kano ya umarceni da nayi maka godiya a bisa biyayya da soyayya da kake masa tun yana Dan maje har ya zama sarki. Wannan abun a yaba makane.
"A bisa haka mai martaba ya umarceni da na sanar da kai ya baka sarautar Sarkin wakar sarkin kano."
Sanarwar ta bayyana cewa za'ayi nadin sarautar mawakin ranar 27 ga watan Disemba a fadar sarkin.
A cikin wata sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram, mawakin wanda tun kafin a nada sarautar ake ma lakabin "sarkin waka" ya yi ma sarkin godiya.
Bayan ya wallafa hoton sarkin ya rubuta "Godiya ta musamman ga mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, Allah ya kara sarki Lpy da nisan kwana."