Rahama Sadau ta gaban kowa a kannywood a Instagram, mabiyan ta sun kai miliyan daya

Rahama Sadau

Jarumar tayi murnar samun yawan mabiya miliyan daya a dandalin sadarwar a makon da ya shude.

Tauruwar fina-finai Rahama Sadau ta sha gaban sauran  fitattun jaruman Kannywood inda ta zama jaruma na farko mai mabiya a shafin Instagram da suka kai miliya daya.

Jarumar tayi murnar samun yawan mabiya miliyan daya a dandalin sadarwar a makon da ya shude.

 

Bisa ga wannan sabon nasarar ita ce na farko a daga masana'antar Kannywood dake da wannan nasarar.

Ta nuna farin cikinta tare da yi dinbim masoyan ta godiya bisa soyayya da.

Jaruman Kannywood dake dap da shiga sahun jarumar sun hada da Hadiza Gabon wanda take da (890,000)  da Ali Nuhu mai mabiya 843,000.

Akwai kuma Nafisa Abdullahi (736,000), Adam A.Zango (738,000), Maryam Booth (685,000).

Post a Comment

Previous Post Next Post