Tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu kuri'u mafi rinjaye na zama gwanin PDP a zaben badi.
Bayan shekara sha biyu yana gwagwarmaya wajen zama gwanin jam'iya na takarar shugaban kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya cinma burin shi inda yayi nasarar zama gwanin babban jam'iyar adawa ta PDP.
Atiku ya doke sauran yan takarar jam'iyar kama daga Rabiu Musa Kwankwso, Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal, Attahiru Bafarawa, Ibrahim Dankwambo, Datti Baba-Ahmed, David Mark, Tanimu Turaki, Jonah Jang, Ahmed Makarfi da Sule Lamido.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu nasarar ne bayan zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar tare da karon kasa a garin Fatakwal babban birnin jihar Rivers wanda ya kama tun ranar Asabar 6 ga wata zuwa washe garin ranar Lahadi 7 ga wata.
Ya samu kuri'u mafi rinjaye cikin da 4,000 da aka kada.
Ga yadda sakamakon zaben ya fito;
Atiku Abubakar - 1532
Aminu Waziri Tambuwal - 693
Bukola Saraki - 317
Rabiu Musa Kwankwaso - 158
Ibrahim Dankwambo - 111
Sule Lamido – 96
Ahmed Makarfi – 74
Tanimu Turaki – 62
David Mark – 32
Jonah Jang – 19
Datti Baba-Ahmed – 5
Kuri'u 68 aka soke a matsayin wadanda basu da amfani.