Tawagar super eagles zata fafata da kasar Seychelles ranar asabar 8 ga watan Satumba daidai karfe 1:30 na rana.
Tawagar yan wasan Super eagles ta Nijeriya na atisaye a kasar Seychelles gabanin wasan su dab kasar ranar Asabar.
Nijeriya zata kara da Seychelles ne a wasan fidda gwani na kofin nahiyar Afrika wanda za'a fara cikin shekarar mai zuwa.
Yan wasan sun garzaya daga kungiyoyin su kai tsaye domin haduwa da sauran yan wasan domin atisaye.
Tsofafi yan wasa da sabbi wadanda suka maye gurbi wasu da suka samu rauni sun hallara a kasar mai tsibiri.
Wasu daga cikin fitattun yan wasan kasar da basu halarci sansanin tawagar sun hada da jagora Mikel Obi da Alex Iwobi wadanda su ji rauni.
Sauran sabbin fuskokin yan wasa da suka samu gayyatar kocin Nijeriya sun hada da Semi Ajayi da Jamilu Collins. Zasu nemi su nuna gwanintar su domin samun damar shiga cikin tawagar asali.
Daya daga cikin sabbin yan wasa da aka gayyata Samuel Kalu wanda ke taka leda a kungiyar Girondins Bordeauxdake kasar Faransa yana mai yakini cewa Nijeriya zata yi iya bakin kokarinta wajen samun nasara a wasan.
Za'a fara wasan daidai karfe 1:30 na ranar Asabar 8 ga watan Satumba.