Shugaban ya dawo ne bayan ziyarar da ya kai birnin Beijing domin halartar taron Forum on China-Africa Corporation (FOCAC) na 2018.
Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya bayan ziyarar kwana shida da ya kai kasar Sin.
Shugaban ya bar kasar ne ranar asabar 1 ga watan Satumba zuwa kasar dake nahiyar Asiya domin hallatar taron gamayyar kasar Sin da Afrika.
A daren ranar Alhamis 6 ga wata jirgin shugaban ya sauka a garin Abuja.
Ya samu tarba yayin da ya sauka daga jirgi daga gwamnoni da wasu yan majalisar dattawa da ma'aikatan majalisar sa.
Cikin su akwai mai girma gwamna Abubakar Muhammed na Bauchi da Gwamna Rochas Okorocha na Imo da Abubakar Badaru na jihar Jigawa.
A bangaren yan majalisa akwai Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Aliyu Magatakarda wamako.
Tags:
Latest Nigerian News