Malaman makarantar Abubakar Tatari-Ali Polytechnic dake jihar Bauchi bata mika wuya ga wannan matakin da kungiyar kwadago tayi, bata amince da tafiya yajin aiki da sauran ma'aikata.
Ma'aikata karkashin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun soma yajin aikin don nuna adawar su ga tsarin biyan albashi mafi karanci da gwamnatin tarayya taki amincewa da zaman ta.
Kungiyar ta fara yajin aiki na wucin gadi wanda zai kai tsawon kwanan bakwai kai ga yadda yarjejeniya ta kasance da gwamnati.
Sai dai kungiyar malaman makarantar Abubakar Tatari-Ali Polytechnic dake jihar Bauchi bata mika wuya ga wannan matakin da kungiyar kwadago tayi, bata amince da tafiya yajin aiki da sauran ma'aikata.
Shugaban kungiyar malaman makarantar Polytechnic (ASUP) na makarantar, Bala Mohammed, ya shaida ewa malaman makarantar ba zasu tafi yajin aiki da NLC ta kaddamar yau Alhamis 27 ga watan Satumba.
Yace malaman dake karkashin kungiyar ASUP basu samu kwararren bayani game da matakin da NLC ta dauka na zuwa yajin aiki.
Ya kara da cewa malaman basu goyi bayan yajin aikin don haka zasu cigaba da gudanar da ayyukan su na koyarwa.
Yayi kira ga daliban makarantar da su koma aji domin karban darasi.
Matakin bijire ma kungiyar NLC da makarantar tayi tana iya jawo ma ASUP biyan haraji ko dakatarwa daga NLC.