Jami'in hulda da mutane na rundunar, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruar hakan yayin da ya zanta da manema labarai.
Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da cewa an sace wasu masu hakar ma'adanai 16 a karamar hukumar birnin gwari.
Kakakin rundunar,DSP Yakubu Sabo, ya shaida ma manema labarai cewa lamarin ya faru daren ranar talata 25 ga watan Satumba.
Yace barayin sun tare motar su yayin da suke kan hanyar komawa gida daga wajen aiki.
Kakakin yace an kaddamar da jami'an sashen hana garkuwa da mutane domin kubutar da ma'aikatan da aka sace.
Ya nuna bakin cikin sa game da faruwar abun takaicin da ya faru, haka zalika ya jaddada cewa jami'an rundunar suna iya bakin kokarin su wajen kubutar da wadanda aka sace da kuma yakinin kama barayin.
Tags:
Latest Nigerian News