Majalisar matan arewa tayi kira ga gwamnatin kasa wajen samad da mafita wajen rage radadin amfani da miyagun kwayoyi tsakanin matan jihohin.
An gano cewa yan matan jihar Kano da Katsina wadanda suka tsinci kansu cikin halin takaicin sune kan gaba wajen amfani da miyagun kwayoyi.
Majalisar matan arewa (NWC) tace karuwar amfani da miyagun kwayoyi cikin al'umma tana faruwa ne bisa halin takaici da rashin ilimi da wasu matan suka tsinci kansu a jihohin Kano da Katsina. Majalisar ta kara da cewa wata sayi tasirin mumunan shawarwari daga abokanan yana haifar da bakan jarabar da ya fado ma al'ummar arewa.
A taron wayar da kai da kungiyar ta gudanar a garin Abuja, kungiyar tayi kira da babban murya ga gwamnatin kasa wajen kawo mafita ga matsaloli dake haifar da amfani da kwaya tsakanin matan arewan.
Shugaban kungiyar Aisha Hussain ta kara da cewa akwai bukatar wayar da kan al'umma wajen kawar da amfani da miyagun kwayoyi tsakanin matan arewa.