Tauraron Super eagles: Ahmed Musa ya koma kasar Saudiya da taka leda

Ahmed Musa

Tsohon kungiyar sa ta Leicester ta amince da yarjejeniyar kungiyar Al-nassr kan fam miliyan 16 na siyan dan wasan Nijeriyan.

Dan wasa mai tauraro Ahmed Musa zai koma kungiyar Al-nassr dake kasar Saudi Arabia da taka leda.

Kungiyar ita tayi nasarar siyan dan wasan bayan tayi da kungiyoyi da dama suka yi domin kawo shi inuwar su domin taka masu leda.

Tsohon kungiyar sa ta Leicester ta amince da yarjejeniyar kungiyar Al-nassr kan fam miliyan 16 na siyan dan wasan Nijeriyan.

Jarumin tawagar yan wasan Super eagles a gasar kofin duniya na bana zai koma kasar larabawa da nuna kwarewansa bisa kwantiragi na tsawon shekaru hudu.

Sabuwar kungiyar da zai koma tayi masa maraba ta hanyar sakon faifan bidiyo da ta wallafa a shafin ta na kafafen sada zumunta.

Ahmed Musa ya bar zakarun gasar firimiya na shekarar 2016 Leicester bayan shekaru biyu da komawa can. Yana daya daga cikin yan wasan da tsohon kocin kungiyar Claudio Ranieri ya siya domin kai farmaki ragar abokan adawar su sai dai dan wasan Nijeriyan bai samu damar nuna bajintar sa a kungiyar sakamakon gwaninta da Jamie Vardy ke nunawa kuma wanda masoyan kungiyar ke alfahari dashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post