Jiga-jigan harkar siyasar jihar Kwara sun koma babban jam'iyar adawa ta PDP.
Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki tare da gwamnan jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed da kakakin jam'iyar APC Bolaji Abdullahi sun dau mataki na barin jam'iya mai mulki.
Jiga-jigan harkar siyasa a jihar Kwara sun koma babban jam'iyar adawa ta PDP.
Bukola Saraki ya fara sanar da ficewar sa a shafin sa na Twitter inda ya jaddada cewa bisa ga wasu dalilai da ya dangaci rashin samun goyon baya daga APC ya dau matakin barin ta zuwa tsohon jam'iyar shi wanda a karkashin ta ya hau karagar shugabancin jiha.
Jim kadan bayan sanarwar tashi gwamnan jihar Sa ya sanar da nashi matsayi ba ficewa daga inuwar APC. Gwamnan yace ya dau matakin ne bayan tattaunawa da shawarwarin da wasu manyan yan siyasa suka bashi na yin haka domin APC ta gaza bashi damar biyan bukatun al'ummar sa.
Shima Sakatare na yadda labarai na APC Bolaji Abdullahi bayi sake ba wajen bin sahun tsohon ubangidan shi.
Yan siyasan sun biyo sahun yan majalisa dokoki sama da 50 hamsin da gwamna da suka sauya sheka.