Mallam Nasir El-rufai: Gwamnan Kaduna ya mika kasafin kudin 2019 ga majalisar dokoki

Kaduna State governor, Nasir El-Rufai

Mallam Nasir El-rufai ya mika kasafin kudin N155BN na 2019 ga majalisar dokokin jiha ranar laraba 15 ga watan Agusta.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai ya mika kasafin kudin 2019 ga majalisar jihar domin neman amincewar majalisar.

Gwamnan da kansa ya mika kasafin kudi na biliyan 155 ga majalisar jihar ranar laraba 15 ga watan Agusta.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta NAN ta ruwaitp, gwamnan yace kasafin ya kasu zuwa kashi biyu, biliyan 63 za'ayi amfani da ita wajen gyare-gyrae yayin da sauran biliyan 92 zata tafi wajen aiwatar da ayyukan cigaba a jihar. Anyi ma kasafin taken "Kasafin cigaba".

Mallam Nasir El-rufai yace kasafin 2019 zata tafi wajen samad da ayyukan cigaban al'umma tare da zuba jari. Ya kara da cewa kashi 42 zata tafi wajen ayyukan walwala. Hakazalika kashi 27.1 zata tafi bangaren ilimi yayin da kashi 15 zata tafi wajen bunkasa harkar lafiya.

Gwaman ya kara da cewa gwamnati zata mayar da hankali wajen karasa ayyukan da ba'a kammala ba a fadin jihar.

Yace gwamnatin jihar zata cigaba da shirin bada ilimi kyuta tare da tabbatar da an samu kwararrun malamai.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post