Ya sanar da hakan ne ranar asabar 4 ga watan Agusta a garin Gombe inda ya bayyana cewa ya daukaka kiran da jama'a suka yi masa na ya fito takarar.
Gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Dankwambo ya fito fili ya sanar da aniyar sa na fitowa takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'oyar PDP.
Ya sanar da hakan ne ranar asabar 4 ga watan Agusta a garin Gombe inda ya bayyana cewa ya daukaka kiran da jama'a suka yi masa na ya fito takarar.
Yace inganta tsaro tare da bunkasa harkar kasuwanci a kasa sune manufofin da zai sama ido inda ya hau karagar mulki.
Hakazalika gwamnan yace zai yi iya bakin kokarin sa ya fatattaki talauci a kasa karkashin shugabanci shi.
A nashi bayyana game da fitowar sa, shugaban cibiyar yakin neman zaben Dankwambo, farfesa Terhember Shinja yace lokaci yayi da dan yankin arewa maso gabas zai maye kujerar shugabancin Nijeriya.
Shugaban yace gwamnan ya taka rawar gani a jam'iyar PDP wajen farfado da martabar ta a idon jama'a.