Ana zargin jami'an sun mamaye harabar ne duk cikin shirin tsige Bukola Sarakin daga mukamin sa na shugaban majalisar dattawa
Labari daga Abuja tana mai tabbatar da cewa jami'an rundunar farar hula ta DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin Nijeriya, sun hana ma'aikata da yan majalisa shiga.
Ana hasashen matakin shiri ne na daukar matakin tsige Bukola Saraki daga mukamin shugaban majalisar dattawa.
Majiyan mu a zauren majalisar sun ruwaito cewa ma'aikata da yan majalisar basu samu damar shiga zauren majalisar inda jami'an suka hana shiga ko fita tare da tare hanyoyi.
An ji dan mjalisar, Sanata Abu Ibrahim yana cewa "Shin ko sojoji sun kwace mulki ne?" yayin da ya tarar da jami'an.
Wani kwakkwarar majiya ya shaida mana cewa jami'an sun tare zauren ne duk cikin matakin tsige shugaban majalisar wanda ya sauya sheka daga APC zuwa PDP ranar 31 ga watan Yuli.
Kawanya da jami'an suka yi ya biyo bayan ganawar da wasu sanatocin APC suka yi shugaban DSS tsakar daren ranar Litinin.
Majiya ya cigaba da cewa APC ya shirin kaddamar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin shugaban majalisar tare da Sanata Hope Uzodinma a matsayin mataimakin sa matukar idan an hana masu rike da matsayin daga shiga zauren yau.