Guguwar sauya sheka: Bolaji Abdullahi ya karyata labarin fitar sa daga APC

The spokesman of the All Progressives Congress (APC), Bolaji Abdullahi has left the ruling party.

A yammacin jiya ne jita-jita ya yadu a kafafen sadarwa na cewa kakakin ya bi sahun tsohon ubangidan sa wajen barin APC bayan da Bukola Saraki ya sanar da matakin yin haka.

Kakakin jam'iyar APC kuma tsohon ministan wasanni Bolaji Abdullahi ya fito fili ya karyata rade-raden da ake yadawa na cewa ya bi sahun shugaban majalisar dattawa wajen sauya sheka daga jam'iya mai mulki.

A yammacin jiya ne jita-jita ya yadu a kafafen sadarwa na cewa kakakin ya bi sahun tsohon ubangidan sa wajen barin APC bayan da Bukola Saraki ya sanar da matakin yin haka.

Yayin da ya zanta da manema labaru a hedkwatar jam'iyar APC dake Abuja yammacin ranar talata, mai magana da yawun APC ya sanar cewa labarin fitar sa daga jam'iyar APC bata da tushe domin har yanzu yana nan daram-dam-dam.

Labarin fitar sa daga APC ya yadu ne sakamakon rashin zuwan sa zaman kwamiti na musamman na jam'iyar da aka saba yi ko wace sati.

"Babu kamshin gaskiya a wannan labarin aje aiki na. Ina son in jaddada cewa babu gaskiya na wannan rahoton. Na fahimce zaton da mutane keyi sakamakon rashin zuwa na zaman kwamitin gudanar da ayyuka ranar litinin. Jama'a basu san cewa na sanar da abokan aiki na cewa na tafi jihar Kwara," yace.

Bugu da kari wasu suna ganin sakamakon kusanci dake tsakanin sa da Bukola Saraki shima zai bi sahun tsohon gwamnan jihar Kwara.

Fangane da fitar Saraki daga APC kakakin yana mai cewa shi bai da niyar barin APC domin "Na shigo ta kofar waje kuma ba zai bar ta ta kofar baya ba."

Post a Comment

Previous Post Next Post