Aikin shaidan: Magidanci mai shekaru 45 yayi luwadi da yaro dan shekara 11 a garin Abuja

Muhammed Sani kenan wanda aka kama yana luwadi da dan shekara 11

Muhammed Sani wanda ake zargi da aikata laifin yana aikin gyaran mota ne kuma ya shafe tsawon watanni da dama yana aikata fasikancin da yaron duk da cewa yana da aure.

Wani magidanci mai shekaru 45 a duniya ya tafka tsiya inda rundunar yan sanda suka kama shi da laifin yi ma wani yaro mai shekaru 11 lalata ta hanyar luwadi a nan unguwar Mabuchi dake Abuja.

Muhammed Sani wanda ake zargi da aikata laifin yana aikin gyaran mota ne kuma ya shafe tsawon watanni da dama yana aikata fasikancin da yaron duk da cewa yana da aure.

Yaron yace ya hadu da wanda ake zargi bayan da wani abokin shi ya hada su domin ya koyi aikin gyran mota a wajen shi. Yace tun lokacin da ya fara zuwa koya aikin ogan sa ke yin lalata dashi kuma bayan ya gama lalata dashi sai ya nashi naira ashirin (N20) na siyan biskit.

Mummunar aikin Muhammed Sani ya bayyana ne bayan da mahaifyar yaron ta gano cewa dan ta ya kan dawo gida fiye da lokacin da aka kayyade masa kuma mafi yawancin tufafin da yasa zuwa aiki ba dashi yake dawowa gida.

Tace a ranar da ta gano cewa akwai lauje daure a cikin zani game da lamarin danta shine ranar da yadawo gida sanye da wando wanda ba nashi ba. Tace sai da ta tasa shi gaba domin ya bayyana inda ya samu wanda kuma menene alakar shi da wanda ya bashi shine ta gano abun dake wakana.

Yayin da yan sanda suke tuhu,mar sa kan laifin da ya aikata Muhammed Sani ya dangane laifin ga aikin shaidan.

"Ba zan iya bayyana mai ya kai ni ga yin haka ba domin ni ba haka nake ba" yace.

Hukumar yan sandan babban birnin tarayya ta Abuja tace zata gurfanar dashi gaban kotu bayan kammala bincike a kan shi domin samun hukuncin da doka ya tanadar ma masu aikata ire-iren laifin da ya aikata.

Post a Comment

Previous Post Next Post