A jihar Zamfara: An kama yan bindiga 20 tare da makamai

Commission dismisses alleged filling of Jigawa quota with non-indigenes

Kwamishnan yace ba za'a sanar da wuraren da aka kama su kuma hukumar baza ta sanar da sunayen su ba bisa ga wasu dalilai na tsaro.

Rundunar yan sandan jihar Zamfara sunyi nasara kama wasu yan bindiga 20 tare da bindigar AK47 guda bakwai.

Kwanmishnan yan sanda ta jihar Kenneth Ebrimson ya sanar da haka yayin da ya zanta da manema labarai a garin Gusau ranar Laraba 15 ga watan Agusta.

Yace dakaru ta musamman daga ofishin shugaban yan sandan Nijeriya tare da hadin gwiwar sauran jami'ai dake sassa daban-daban suka yi nasara kama yan bindigar.

Kwamishnan yace ba za'a sanar da wuraren da aka kama su kuma hukumar baza ta sanar da sunayen su ba bisa ga wasu dalilai na tsaro.

Ya kara da cewa bisa ga tsatsaurar mataki da rundunar ta dauka wajen fatattaki yan bindigar akwai yiuwar samun galaba cikin yan kwanakin nan.

A bisa bayanin sa, rundunar ta kaddamar da dakaru masu sintiri domin rage tashin hankali da cece-kuce dake yaduwa game da tsaro tare da kama wadanda ke haifar da tarzoma.

Daga karshe ya shawarci al'ummar jiha da su taimaki jami'an tsaro da duk wata labari da zai taimaka wajen kawoi karshen ta'adanci ko sace-sace a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post