A garin Kaduna: Masu garkuwa da mutune sun sace Sheikh Al-garkawi

Sheikh Ahmad Al-garkawi

Masu garkuwan sun sace shehin malamin ne a dai dai gonar makarantar sa dake wajen garin Kaduna.

Labarin daga jihar Kaduna na tabbatar cewa wasu barayi sun sace shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Al-garkawi tare da wasu dalibansa.

A labarin da jaridar Dessert herald ta fitar yan bindigan sun sace shehin Malamin tare da dalibansa ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, a daidai lokacin da suka kai ziyara gonar makarantarsa dake wajen garin Kaduna.

Wani daliban sa mai suna Mallam Lawal ya tabbatar ma yan jarida da aukuwar al’amari inda yake cewa malamin ya tafi gonar sa ne dake Unguwar Nariya tare da wasu daga cikin daliban sa da a nan ne suka gamu da masu garkuwan.

Tun ba yau ba al'ummar jihar Kaduna kai fama da hare-haren yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane. Batun sace malamin ya biyo bayan matakin tsawaita tsaro da gwamnati ta dauka domin kawo karshen tarzomar da jama'a ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post