Tsaron Sambo Dasuki: Ministan Shari'a Malami yace da sa hannun Dasuki wajen mutuwar yan Nijeriya 100,000

Mohammed Sambo Dasuki listens to a question after his address at Chatham House in London, January 22, 2015. REUTERS/Andrew Winning

Ministan yace gwamnatin tarayya baza ta saki Dasuki domin tuhumar da ake masa ya shafin al'ummar kasa.

Babban ministan shari'ar Nijeriya Abubakar Malami yace tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki yana da hannu game da mutuwar mutum 100,000.

Ministan ya bayyana dalilin da yasa gwamnati ta cigaba da tsaron Dasuki duk da umarnin da kotu ta bada yayin da ya zanta da wakilin sashen hausa na VOA.

Tsohon sojan yana fuskantar tuhuma kan zargin wawure kudin makamai da aka ware domin yakar mayakan Boko haram a cikin 2015.

A zaman kotu da aka gudanar kan zargin ranar litinin 16 ga watan Yuli, babban kotun tarayya dake gudanar da zaman ta a birnin tarayya ta bashi damar yin beli kan zargin da ake masa.

Duk da cewa wannan shine karo na shidda da kotu zata bashi damar yin haka, har yanzu tsohon hadimin tsohon shugaban kasa na cigaba da fuskantar tsaro a gidan wakafi.

Malami yace gwamnatin tarayya baza ta saki Dasuki domin tuhumar da ake masa ya shafin al'ummar kasa.

A hirar sa, alkalin ya bayyana cewa hakkin Dasuki bata kai ga na mutum 100,000 da ake zargi da sa hannun sa wajen rasuwar su.

Ministan ya kara da cewa rashin kulawa da yanda ake kashe kudi karkashin inuwar tsohon hadimin yayi sanadin mutuwar jami'an sojoji da dama.

Yace gwamnati Shugaba Muhammadu Buhari tana mutunta tsari doka da umarninta amma idan batun da ake la'akari akanta ya shafi jama'ar kasa toh ba za'a lura da hakkin mutum daya tilo.

Post a Comment

Previous Post Next Post