Siyasar Kano: Tsofaffin abokan hamayya Kwankwaso da Shekarau sun gana

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Malam Ibrahim Shekarau

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa hoton su tare a shafin sa na Twitter tare da rubuta cewa suna gina yadda zasu samad da cigaba a Nijeriya.

Tsofaffin abokin hammaya a harkar siyasa na jihar Kano kuma tsofaffin gwamnonin jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau sun gana bayan shekaru da dama da yin haka.

Jiga-jigan sun gana ne ranar asabar 28 ga watan Yuli a gidan Shekarau dake nan unguwar Asokoro na garin Abuja bayan Sanata Kwankwaso ya sauya sheka zuwa PDP inda Shekarau yake.

Wannan shine karo na farko da tsofafin abokan hamayya zasu gana bayan wanda suka yi a cikin shekarar 2003 inda Kwankwaso ya mika ma Shekarau mulkin jihar Kano bayan ya fadi zabe.

Malam Ibrahim Shekarau yace maraba da komawar takwaransa zuwa jam'iyar PDP.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa hoton su tare a shafin sa na Twitter tare da rubuta cewa suna gina yadda zasu samad da cigaba a Nijeriya.

 

A labarin da BBC ta fitar gabanin ganawar tasu, Mallam Ibrahim Shekarau ya jaddada cewa sun dade suna fatan Kwankwaso ya dawo PDP.

Yana mai cewa "Duk wani dan siyasa yana son kari ko da mutum daya ne, kuma mu wannan tagomashi ne gare mu."

"Ana cin zabe da kuri'a daya ana faduwa da kuri'a daya. mutanen da Kwankwanso ya zo da su karuwa ce ga PDP duk da cewa ba duka za su bi shi ba."

Game da batun wa zai jagoranci jami'iyar a jihar Kano tsohon gwamnan yana mai cewa "Ba wani ne yake nadi ba na jagora, idan tsarin jam'iyya za a bi, yanzu batun wanene jagora duk bai taso ba."

"Kwankwaso yana sahun gaba cikin manyan iyayen jam'iyya, idan mun fahimci juna da shi mun zama iyayen jam'iyya muna tare, kuma kafadarmu daya."

Ya kara da yin watsi da rade-raden dake yawo na cewa zai koma APC. Yace bai taba yin zancen ba kuma babu wani jami'in jam'iyar APC da ya zo masa da zancen.

Post a Comment

Previous Post Next Post