Jagoran al'ummar jihar Benuwe ya bayyana cewa ya dauki matakin ficewa da APC ne bisa ga reshin jituwa dake tsakanin sa da shugaban jam'iyar na jihar.
Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom yayi na maza inda ya yanke shawarar barin jam'iyar APC zuwa PDP.
Gwamnan ya dauki wannan matakin bayan yan kwanaki da nuna alamun yin haka. A kwanan baya ne gwamnan ya sanar da cewa zai fice daga jam'iyar mai mulki sai dai amma bai sanar da inda zai koma ba.
Jagoran al'ummar jihar Benuwe ya bayyana cewa ya dauki matakin ficewa da APC ne bisa ga reshin jituwa dake tsakanin sa da shugaban jam'iyar na jihar.
Tuni dai matasan jihar suka jinjina masa bisa matakin da ya dauka na barin APC.
Wata kungiyar matasa mai suna Benue Youth Alliance for Ortom (BYAFO) tayi maraba da hukuncin da ya dauka a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar.
Jagoran kungiyar Lorliam Shija ya sanar cewa hakan na nuna cewa gwamnan ya amsa kiran da al'ummar sa suka yi masa.
Yace matasan jihar sun goyi bayan matakin da ya dauka dari bisa dari kuma hakan zata taimaka cinma manufar samad da cigaba a jihar.
Daga karshe jagoran kungiyar BYAFO yayi kira ga sauran al'ummar jihar da su mara ma gwamnan baya domin cinma manufar shi.