Hukumar tace ma'iakatan da zata dauka aiki sun hada da matasa masu yi ma kasa hidima ta shirin NYSC da daliban manyan makarantun kwaleji da ma'aikatan ma'aikatar gwamnatin tarayya da na jihar Katsina.
Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta INEC tace akalla ma'aikata 7,727 zata dauka aikin sake zaben takarar majalisar dattawa a Jihar Katsina.
Hukumar zata sake gudanar da zaben dan majalisar dattawa a jihar sakamakon rasuwar tsohon dan majalisa Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu cikin watan Afirilu na bana.
Marigayin ya rasu ne ranar 4 ga watan Afirilu bayan wata gajeruwar rashin lafiya da yayi jinya.
A labarin da NAN ta ruwaito, za'a sake zaben donneman wanda zai maye gurbin marigayin a zauren majalisar tarayya.
A jawabin sa wajen taron da hukumar ta shirya da al'ummar jihar ranar alhamis 19, kwamishnan hukumar na jihar Katsina Jibril Ibrahim-Zarewa yace an baiwa hukumar kwana talatin don sake gudanar da zaben majalisa a jihar.
Yace hakan ya biyo bayan wasikar da fadar majalisar dattawa ta turo ma hukumar ranar 13 ga watan yau. A cewar sa INEC tana da damar gudanar da zaben tsakanin ranar 13 ga wata da suka amshi sakon zuwa ranar 12 ga watan Agusta domin gudanar da zaben.
Kwamishna ya kara da cewa ma'aikatan da za'a dauka aikin zaben sun hada da matasa masu yi ma kasa hidima na shirin NYSC da daliban jami'a da manyan makarantu da kuma ma'aikatan ma'aikatar tarayya da sauran ma'aikatun jihar Katsina.
Ibrahim Zarewa yace hukumar zata yi amfani da na'ura wajen tantance masu zaben.
Mazabar da kujerar da za'a takarar sa sun hada da karamar hukumar Baure, Bindawa, Daura, Dutsi, Ingawa, Kankia, Kusada, Mai’adua, Mani, Mashi, Sandamu da Zango.
Ya bayyana cewa mutum 23,105 suka yi rejistar zaben ciki mutum 6,066 suka amshi shaidar katin gudanar da zabe yayin da ake neman sauran 15, 892.
Daga karshe yayi kira ga yan siyasa da kafofin watsa labarai da shugabannin al'umma da addinin da sauran jama'ar jihar da su basu goyon baya domin gudanar da zaben cikin lumana.