
Ta kara da cewa da farko dai ta dauki abun da wasa amma daga baya ta gane cewa labarin mutuwarta ya yadu sosai duba da yawan mutane da suka kira ta.
Tsohuwar fitacciyar jarumar dandalin wasan kwaikwayo, Sadiya Gyale ta fito ta karyata mutuwarta da aka ringa yadawa a kafafe sada zumunta makon da ya shude.
Daya daga cikin fuskokin da suka raya masana'antar fina-finan hausa ta Kannywood, tace lamarin ya bata mamaki.
Hirar ta da wakilin BBC kan lamarin, tsohuwar tauraruwa ta bayyana cewa ita dai lafiyan ta kalau. Tace tana zama-zaman ta ringa samun kiraye-kiraye daga yan uwa da abokan arziki don tabbatar da lamarin.
Ta kara da cewa da farko dai ta dauki abun da wasa amma daga baya ta gane cewa labarin mutuwarta ya yadu sosai duba da yawan mutane da suka kira ta.
Sai dai jarumar ta ce hankalin ta bai tashi ba bayan faruwar hakan domin ta san cewa wata rana duka mai rai zai zama mamaci. Ta tabbatar ma daukacin masoyanta cewa tana nan da ranta cikin koshin lafiya.
Sadiya Gyale, ta ce a gaskiya yada ire-iren wadannan labarai na karya sam ba dai-dai ba ne a cikin al'umma musamman musulmai.
Ta ce "A gaskiya duk wanda ko wadda ta shirya wannan labari, to ta daukarwa kanta ko kansa babban alhaki, kuma ba bu wata riba da mutum zai samu a kan hakan."
Daga karshe tace ta goyi bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka kan masu yada labaran karya a kafafen sada zumunta.