Rikicin jihar Filato: Shugaba Buhari zai karrama limamin da ya ceci rayuwar mutane 300

Buhari to give Imam who saved lives in Plateau national honour

Limamin ya ceci rayuwar su ta hanyar boye su a cikin masallacin yayin da rikici ya barke a jihar Filato kwanan baya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhariu zai karrama jarumin limami Abdullahi Abubakar da ya ceci rayuwar mutane akalla 300 yayin da ya rikici barke a jihar Filato kwanan baya.

Shugaban ya gayyaci malamin fadar shi inda zai karrama shi da lambar yabo na musamman bisa bajinta da ya nuna na ceto rayukar mutane wadanda mafi yawancin su kiristoci ne

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya sanar da wannan matakin da shugaban zai dauke a wajen taron kwana uku na tattaunawa kan hanyar samad da zaman lafiya da tsaro da aka shirya a garin Jos.

Rikicin da ya barke  a ranar 23 da 24 na watan Yuni a garin Barkin ladi tsakanin makiyaya da manoma yayi sanadin rayuka akalla 100.

Limamin mai shekaru 83 a duniya ya ceci rayuka yan gudun tsira yayin da suka nemi mafaka a kauyen Ghashi. Ya boye su a gidansa da masallaci da yake jagorantar sallah.

Mafi yawanci wadanda ya ceto yan kabilar Berom ne kuma kiristoci.

Yayin da ya zanta da wakilin BBC Pidgin, limamin yace "Na boye yan matan a gidana kana na boye mazajen a masallaci."

Limamin yayi karya ga wadanda suka biyo su har inda suka boye inda ya sanar masu cewa su duka musulmai ne kuma ya roke su da su bar shi da mutanen sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post