Ministan harkokin zirga-zirgar jirgin sama Hadi Sirika ya kaddamar da sabuwar jirgin saman nijeriya a wani taron baje kolin jiragen sama a Farnborough na birnin Londan nan Birtaniya.
Bayan shekaru da dama da durkushewar ta, gwamnatin Nijeriya ta kaddamar sabuwar fuskar kamfanin jirgin saman kasa.
Ministan harkokin zirga-zirgar jirgin sama Hadi Sirika ya kaddamar da sabuwar jirgin saman nijeriya a wani taron baje kolin jiragen sama a Farnborough na birnin Londan nan Birtaniya.
Bayan shekara 15 da kulle kamfanin, an sauya sunan ta daga "Nigerian Airways" zuwa "Nigeria Air".
Ministan yace ana sa ran zuwa watan Disamban Bana kamfanin zai fara aiki gadan-gadan kuma jiragen ta zata ringa zirga-zirga kashi uku zuwa kasashe 81 na daga cikin gida da kasashen Afrika ta yamma da ma sauran kasashen duniya.
Batun farfado da kamfanin jirgin saman nijeriya ya tabbata ne bisa hadin gwiwar yan kasuwa. Ministan yace ita ce hanyar da tafi dacewa da za'a dauki lokaci ana cin moriyarsa.
Gwamnatin Nijeriya tana da kaso 5 cikin 100 na daga cikin kamfanin kuma bata da iko wajen tafiyar da alamuran ta ko yin gyara.
Yan Nijeriya sun jinjina ma Gwamnati
Matakin farfado da kamfanin Nijeriya ya haifar da abun muhawara a kafafen watsa labarai da dandalin sada zumunta.
Jim kadan bayan kaddamar da sabuwar fuskar kamfanin da kuma ranar da zata fara aiki al'ummar Nijeriya da dama sun yaba wa gwamnatin tarayya bisa rawar da ta taka wajen farfado da kamfanin.
Wasu na ganin cewa farfado da kamfanin zai taimaka wajen rage farashin jigilar mutane ta jirgin sama tare da tafiya zuwa sassa daban-daban wanda ke ci ma kamfanunukar yan kasuwa tuwo a kwarya wajen isar ta.
Haka zalika wasu na da ra'ayin cewa kamfanin zai taimaka wajen rage wahalhalu da ake sha wajen tafiye-tafiye.
A can baya Najeriya tana da kamfanin Nigeria Airways da ke zirga-zirga a kasar har zuwa kasashen waje, amma kamfanin ya durkushe saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma'aikata.
Durkushewar kamfanin ya haifar da rasa ayyukanyi ga ma'aikata da dama.