Mesut Ozil: Shaharraren dan wasa yayi murabus bayan cin mutunci da ya fuskanta daga yan kasa

Ozil, 29, came in for stinging criticism in Germany for their shock first-round defeat at the World Cup

Yace ya dau matakin ne ba don yayi niyar yin haka ba sai dai don kare mutuncin sa bayan rashin girmamawa da yan kasar suka nuna mashi game da asalin sa.

Fitaccen dan wasan kwallon kafan kasar Jamus, Mesut Ozil ya dau mataki na daina taka leda da tawagar yan wasan kasar bayan musgunawan da ya fuskanta daga yan kasar.

Labarin daukar wannan matakin ya fita a ne wata sanarwa da dan wasan ya wallafa a shafin sa na kafafen sada zumunta ranar Lahadi 22 ga watan yuli.

Yace ya dau matakin ne ba don yayi niyar yin haka ba sai dai don kare mutuncin sa bayan rashin girmamawa da yan kasar suka nuna mashi game da asalin sa.

 

Dan wasan wanda asalin sa dan kasar Turkiya ne amma an haife shi a kasar Jamus ya gamu da rashin jituwa da yan kasar Jamus sakamakon hoton da yayi da shugaban kasa Tayyip Erdogan gabanin gasar kofin duniya wanda aka yi a kasar Rasha.

Ozil yana daga cikin tawagar yan wasan kasar da suka yi nasarar lashe gasar kofin duniya a shekarar 2014 kuma yana daya daga cikin yan wasan da suka taka rawar gani a  tarihin yan wasan kasar.

Ya fuskancin cin mutunci daga yan kasar bayan wani hoto da yayi da shugaban kasar Turkiya a cikin watan Mayu na wannan shekarar.

kamar yadda rahotanni  da jama'ar kasar suka dauki hoton ana zargin dan wasan da nuna fifiko zuwa asalin kasar mahaifin sa.

Lamarin dai ya kara kamari bayan da tawagar yan wasan kasar suka fuskanci zagon kasa a gasar bana inda suka fice daga gasar ba tare da sun kai zagaye na biyu ba.

 

Kamar yadda ya sanar a cikin sakon da ya fitar dan wasan yace yan kasar basu girmama shi ba dangane da asalin sa bisa yadda suke lika masa alhaki kan rashin nasarar tawagar kasar a gasar wannan shekarar.

Ya danganta lamari da rashin adalci da nuna wariya da bambanci kasancewa asalin sa na da dangantaka da Turkiya.

Yace idan tawagar tayi nasara alhakin yana kan ko wani dan wasa amma idan aka samu sabanin haka sai a daura masa alhakin a matsayin sa na bakin haure.

Ya nuna bacin ransa ga hukumar kwallon kafar kasar

Dan wasan mai shekaru 29 yace hukumar kwallon kafa na kasar karkashin jagorancin Reinhard Grindel. bata yunkura wajen kare mutuncin sa yayin da lamarin ya zama a abun muhawara a kafafen watsa labarai.

Labarin hoton nasa ya mamaye kafafen sada zumunta kuma ya zama abun muhawara a kafafen watsa labarai inda masu sharhi suke ta sukar shi kan nuna kauna ga kasar mahaifan sa.

Yace shugaban hukumar yayi amfani da lamarin wajen cin wani manufa ta harkar siyasa wanda bata da alaka da sana'ar shi.

Hoton da ta tada kura a kasar shine wanda dan wasan tare da abokin sa na tawagar yan wasan Jamus Ilkay Gundugan da dan wasan Everton kuma dan kasar Turkiya Cenk Tosun suka yi tare da shugaban kasar Turkiya a birnin London gabanin zaben kasar.

 

fadar shugaban ta wallafa hoton a shafin ta na yanar gizo da Twitter kwanaki kadan gabanin zaben wanda Erdogan ya lashe.

An dangakata haduwar da wani mataki na yin kamfe duba da irin goyon baya da yan wasan suke samu daga dinbim masoyan su masu bin harkar kwallon kafa.

Shi dai Ozil yace duk da cewa a dai dai lokacin da suka dauki hoton batun zabe na kamari yace basu yi shi ba don cinma manufar siyasa ko zabe, yayi shine don girmama martabar kasar iyayen sa.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post