Yan bindigar sun kai harin ne a kauyyuka 18 dake karkashin gundumar Mashema, Kwashabawa da Birane na karamar hukumar Zurmi ranar Juma'a 27 ga watan Yuli.
Har yanzu alummar jihar Zamfara na fuskantar fargaba inda wasu yan bindiga suka kai sabuwar hari wanda yayi sanadin mutuwar akalla mutane 42.
Yan bindigar sun kai harin ne a kauyyuka 18 dake karkashin gundumar Mashema, Kwashabawa da Birane na karamar hukumar Zurmi ranar Juma'a 27 ga watan Yuli.
Wani shaida ya bayyana ma manema labaru cewa adadin mutane da suka rasu zasu kai 100 yayin da mutane da dama ba'a san inda suka shige ba.
A labarin da jaridar Daily Nigerian ta fitar, yan bindigar sun halaka gidaje da dama sakamakon harin da suka kai.
Wani mazaunin kauyen Lawalli Mashema ya bayyana cewa daruruwan mutanen garin da harin yan bindiga ya shafa suka kaurace zuwa birnin Zurmi wanda ya kai kilomita 50 daga kauyukan.
Ya kara da cewa wasu kuma sun kaurace zuwa jihar Katsina yayin da wasu kuma suka nufi jamhoriyar Nijar don neman mafaka.
A yayin da ya ziyarci garin da lamarin ya faru, mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Wakkala ya Allah wadai da mummunar harin da ya faru.
Yace gwamnati zata dau mataki cikin gaggawa game hare-haren dake faruwa a jihar.
Shima kakakin majalisar dokoki na jihar Sanusi Rikkiji yayi kira ga hukumomin tsaro kan a inganta harkar tsaro a yankin.
Al'ummar jihar Zamfara na fuskantar zamanm dar-dar sakamakon hare-haren da yan bindiga kai kaiwa jihar wanda yayi sakamkon mutuwar daruruwan mutane tare da sa wasu da dama kauracewa zuwa garuruwa da jihoji dake makwabtaka dasu domin neman tsira.
Mummunar hare-haren na cigaba da faruwa duk da albishirin da shugaba Muhammadu Buhari yayi ma al'ummar jihar yayin da ya kawo musu ziyara na daukar matakin tsawaita tsaro.