Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari ya gana da yan majalisar datawan APC a fadar sa

Shugaba Buhari tare da sanata Shehu Sani a wajen taron tattaunawa da yan majalisar APC suka yi da shugaban a fadar sa

Daya daga cikin yan majalisar dattawan da suka gana da shugaban Sanata Shehu Sani ya bayyana wa manema labaru bayan ganawar tasu cewa sun tattauna kan batutuwa masu muhimmanci da dama.

Bayan matakin ficewa daga jam'iya mai mulki da wasu sanatoci suka yi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da sauran yan majalisar dattawa da suka cigaba da amsa kiran APC.

Shugaban ya gana da yan majalisar ne a fadar sa daren ranar laraba 25 ga wata inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwa domin dakile duk wata rikici da jam'iyar ke fuskanta.

 

Ganawar sirri da suka gudanar ya biyo bayan wasu sanatoci 15 daga APC suka sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP da ADC bisa ga wasu matsaloli da suke kalubalantar uwar jam'iyar da haifarwa.

Daya daga cikin yan majalisar dattawan da suka gana da shugaban Sanata Shehu Sani ya bayyana wa manema labaru bayan ganawar tasu cewa sun tattauna kan batutuwa masu muhimmanci da dama.

Dan majalisar mai wakiltar jihar Kaduna yace cikin batutuwan da suka tattauna a kai akwai batun halin da yan majalisar APC ke ciki a zauren majalisar tarayya tare da rikice-rikice da ya faru a jam'iyar wanda ya jawo har wasu suka fice zuwa wata jam'iya.

 

Shehu Sani ya kara da cewa bayan tattaunawar da suka yi da shugaban a kan wannan batutuwan shugaban yayi masu alkawarin yin iya bakin kokarin sa wajen kawo karshen matsalolin da jam'iyar ke fuskanta.

Shugaban, ya kuma yi bayanin cewa, mafi yawancin sanatocin da suke da matsala da jam'iyyar ta su, rikice-rikicen jihohi ne ya haddasa hakan, don haka ya yi alkawarin shiga tsakani don kawo karshen hakan.

 

Sanatan ya daura da cewa zasu hada kai da shugaban inda suka shigar da wani kudurin da zai taimaka wajen hada kan yayan jam'iyar domin cin nasarar a zabe mai zuwa.

Bugu da kari sanatan yace kudurin zata tabbatar da amince da duk wani hukunci da jam'iyar ta zana ga ko wani zababben gwamna ko dan majalisa.

Taron ya samu halarcin shugaban jam'iyar APC Adams Oshiomole da sauran ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post