Yace mutum 18 kenan aka kama dangane da kashe-kashen da ya faru kuma za'a mika su ga hukumar yan sanda domin kara bincike gabanin gurfanar dasu gaban kotu.
Jami'an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargin cewa da hannun su a rikicin da ya faru a karamar hukumar Barkin ladi da Riyom na jihar Filato wanda yayi sanadin rasa rayuka sama da 200.
An bayyana wadanda ake zargin a shelkwatar dakarun Operation Safe haven dake garin Jos ranar talata 17 ga watan Yuli.
Shugaban cibiyar watsa labarai na rundunar sojojin Nijeriay, Birgediya Janar John Agie ya tabbatar da faruwar haka inda ya jaddada cewa dakarun rundunar suna cigaba da bincike domin kama wadanda ke da hannu a rikicin da ya faru ranar 23 ga watan Yuni.
Yace mutum 18 kenan aka kama dangane da kashe-kashen da ya faru kuma za'a mika su ga hukumar yan sanda domin kara bincike gabanin gurfanar dasu gaban kotu.
Tags:
Latest Nigerian News