
Yan wasan tawagar sun nuna bajinta da kwarewa gabanin kammala wasan. Antoine Grizman, Paul Pogba da Kylian Mbappe suka zura kwallo a ragar Croatia.
Bayan shekaru 20, kasar Faransa ta kuma yin nasarar zama zakarun duniya a gasar kofin duniya ta 2018 wanda ta gudana a kasar Rasha.
A cikin shekarar 1998 kasar tayi nasara lashe kofin gasar na farko kuma kocinta na yanzu ya daga kofin tare da sauran yan wasan tawagar a shekarar. Bayan shekara 20 ya kuma jagoranci yan wasan wajen sake lashe kofin gasar.
Wasan ta na karshe da kasar Croatia, France ta doke abokan adawar su da ci 4-2 a wasan wanda aka buga a filin kwallo ta Luzhniki ranar lahadi 15 ga watan Yuli.
Yan wasan tawagar sun nuna bajinta da kwarewa gabanin kammala wasan. Antoine Grizman, Paul Pogba da Kylian Mbappe suka zura kwallo a ragar Croatia.
Kwallayen da Perisic da Mario Mandzukic suka zura a ragar mai tsaron gidan Faransa bai ka ga samun galaba ba ga tawagar kasar mai adadin mutum miliyan 4.
Abun mamakin game da tawagar da suka yi nasarar a gasar shine, shine yadda matashin dan wasa Mbappe ya taka rawar gani wajen daga tambarin Faransa a duniya.
Matashin dan kwallo shine na farko bayan shahararren tsohon dan wasan Brazil, Pele, wanda zai zura kwallo a ragar abokan adawa a wasan karshe na gasar mai shekaru kasa da 20.
Wasan dai ya samu halarci daga shugaban kasar Rasha, Vladamir Putin da shugaban kasar zakarun gasar, Emmanuel Macron da shugaban kasar Croatia, Kolinda Grabar-Kitarović.
Shugaban Faransa wanda ya ziyarci Nijeriya kwanan baya ya kasa boye farin cikin sa bisa nasarar da kasara sa ta samu. An gan yadda yake taya yan wasan farin ciki tare da rungume su yayin da bada tambarin nasara na lashe kofin bana.
Sauran bakin da suka halarci wasan karshen sun hada da tsofaffin fitattun yan wasan kwallo da manyan yan siyasa.
Yadda Faransa ta kaya a gasar 2018
Ga yadda Zakarun bana suka kaya a wasannin gasar bana tun daga rukuni har ga zagayen karshe:
Faransa 2-1 Australia
Faransa 1-0 Peru
Denmark 0-0 Faransa
Zagaye na farko
Faransa 4-3 Ajentina
Zagaye na biyu
Faransa 2-0 Uruguay
Wasan daf da karshe
Faransa 1-0 Belgium
A wasa na karshe Faransa ta doke Croatia da 4-2.