Bukola Saraki: Yadda jami'an tsaro suka yi ma gidan shugaban majalisa kawanya

Yan sanda sun tare hanyoyin shiga layin gidan Bukola Saraki

Mataimakin sa majalisar Bamikole Omisore ya sanar da faruwar haka a shafin sa na Twitter tare da hotunan yadda yan sandan suka tare hanyoyi.

Jami'an rundunar yan sanda sunyi ma gidan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kawanya.

Jami'an sun tare duka hanyoyin shiga layin gidansa dake unguwar Maitama nan garin Abuja.

Mataimakin sa majalisar Bamikole Omisore ya sanar da faruwar haka a shafin sa na Twitter tare da hotunan yadda yan sandan suka tare hanyoyi.

 

Saraki ya sake shiga tarkon rundunar yan sandan bayan sammaci da rundunar ta fitar kan a sake tuhumar shi kan barayin garin Offa da aka kama wadanda suka bayyana cewa shi ke goya masu baya.

Kamar yadda hadimin sa ya sanar yan sandan sun tare shi ne yayin tafiya shelkwatar rundunar gomin amsa gayyatar da sufeton yan sanda ya tura masa kan batun barayin garin Offa.

Kai ga yanzu rundunar yan sanda bata fitar da wani bayani game da batun kawanya gidan shugaban majalisar.

A wani bangare kuma mun samu labari cewa, jami'an hukumar EFCC sun mamaye gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, dake nan unguwar Apo tun da asuba.

Wannan ya fito a ciki wata rahoto da BBC ta fitar.

Batun na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman yan murna tsakanin Sanata Saraki da wasu gaggan 'yan jam'iyyar ta APC da kuma bangaren Shugaba Muhammadu Buhari.

Sun dai zargi shugaban da ci musu zarafi da kuma nuna musu banbanci, lamarin da ya kai ga wasunsu yin bore da kafa na su jam'iyyar wanda ake kira da rAPC karkashin jagorancin Alhaji Buba Galadima.

Post a Comment

Previous Post Next Post