Atiku Abubakar: Tsohon mataimakin shugaban kasa yace zai yi maganin Boko haram idan yaci zabe

Let June 12 inspire promotion of democratic principles

Tsohon dan siyasan ya bayyana hakan yayin da yake jawabin a taron da yayi da magoya bayan jam'iyar PDP a jihar Borno.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai kawo karshen ta'adancin boko haram idan yaci zaben shugaban kasa.

Ya sha alwashin yin maganin rikicin yan ta'adda da rikicin makiyaya da manoma dake faruwa a kasa cikin kankanin lokaci idan ya hau kujerar mulkin kasa.

Tsohon dan siyasan ya bayyana hakan yayin da yake jawabin a taron da yayi da magoya bayan jam'iyar PDP a jihar Borno.

A taron wanda aka gudanar ranar Talata 17 ga wata a dakin taro na Forshams Hall dake Maiduguri, jigon jam'iyar PDP yace gwamnatin sa baza tayi jinkiri ba wajen kawo karshen ta'adanci duba da irin asarar da suka janyo a yankin arewa maso gabas.

Yace ta'adanci tana da alaka da talauci don haka zai yi iya bakin kokarin sa wajen kawo karshen talauci a yankin.

A cewar sa rikicin makiyaya da manoma ta cigaba ne bisa ga rashin shugabanci nagari.

Yayi kira ga dinbim magoyan jam'iyar da yan Nijeriya dasu taimaka wajen fitar da jam'iyar APC daga karagar mulkin kasa.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post